لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبۡهُ عَذَابًا أَلِيمٗا

Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, (Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi.


۞لَّقَدۡ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ يُبَايِعُونَكَ تَحۡتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَثَٰبَهُمۡ فَتۡحٗا قَرِيبٗا

Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci.


وَمَغَانِمَ كَثِيرَةٗ يَأۡخُذُونَهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Da waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa da zã su karɓo su. Kuma Allah Yã kasance Mabuwayi, Mai hikima.


وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةٗ تَأۡخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمۡ هَٰذِهِۦ وَكَفَّ أَيۡدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُمۡ وَلِتَكُونَ ءَايَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَيَهۡدِيَكُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta muku wannan. Kuma Ya kange hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.



الصفحة التالية
Icon