Al-Hujurat
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da ManzonSa. Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَرۡفَعُوٓاْ أَصۡوَٰتَكُمۡ فَوۡقَ صَوۡتِ ٱلنَّبِيِّ وَلَا تَجۡهَرُواْ لَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ كَجَهۡرِ بَعۡضِكُمۡ لِبَعۡضٍ أَن تَحۡبَطَ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصۡوَٰتَهُمۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱمۡتَحَنَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡ لِلتَّقۡوَىٰۚ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٌ
Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِن وَرَآءِ ٱلۡحُجُرَٰتِ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ
Lalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali.