وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱخۡتَلَفُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma.
يَوۡمَ تَبۡيَضُّ وُجُوهٞ وَتَسۡوَدُّ وُجُوهٞۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسۡوَدَّتۡ وُجُوهُهُمۡ أَكَفَرۡتُم بَعۡدَ إِيمَٰنِكُمۡ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱبۡيَضَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فَفِي رَحۡمَةِ ٱللَّهِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Kuma amma waɗanda fuskõkinsu suka yi fari, to sũ suna cikin rahamar Allah kuma, su a cikinta, madawwama, ne.
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۗ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعَٰلَمِينَ
Waɗannan ãyõyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya, kuma Allah bã Ya nufin wani zãlunci ga tãlikai.
وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra.