وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ يَسۡتَغۡفِرۡ لَكُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ لَوَّوۡاْ رُءُوسَهُمۡ وَرَأَيۡتَهُمۡ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ

Kuma idan aka ce musu "Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara," Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai.


سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ أَسۡتَغۡفَرۡتَ لَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ لَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba.


هُمُ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُواْ عَلَىٰ مَنۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ حَتَّىٰ يَنفَضُّواْۗ وَلِلَّهِ خَزَآئِنُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَفۡقَهُونَ

Sũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta.


يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعۡنَآ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ لَيُخۡرِجَنَّ ٱلۡأَعَزُّ مِنۡهَا ٱلۡأَذَلَّۚ وَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."



الصفحة التالية
Icon