وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ لَكُمۡ وَلِتَطۡمَئِنَّ قُلُوبُكُم بِهِۦۗ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Kuma Allah bai sanya shi ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.


لِيَقۡطَعَ طَرَفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡ يَكۡبِتَهُمۡ فَيَنقَلِبُواْ خَآئِبِينَ

Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi.


لَيۡسَ لَكَ مِنَ ٱلۡأَمۡرِ شَيۡءٌ أَوۡ يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡ أَوۡ يُعَذِّبَهُمۡ فَإِنَّهُمۡ ظَٰلِمُونَ

Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne.


وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.


يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُواْ ٱلرِّبَوٰٓاْ أَضۡعَٰفٗا مُّضَٰعَفَةٗۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.



الصفحة التالية
Icon