فَٱنقَلَبُواْ بِنِعۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضۡلٖ لَّمۡ يَمۡسَسۡهُمۡ سُوٓءٞ وَٱتَّبَعُواْ رِضۡوَٰنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَظِيمٍ

Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma.


إِنَّمَا ذَٰلِكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ يُخَوِّفُ أَوۡلِيَآءَهُۥ فَلَا تَخَافُوهُمۡ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni.


وَلَا يَحۡزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡكُفۡرِۚ إِنَّهُمۡ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۚ يُرِيدُ ٱللَّهُ أَلَّا يَجۡعَلَ لَهُمۡ حَظّٗا فِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.


إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلۡكُفۡرَ بِٱلۡإِيمَٰنِ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi.


وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّمَا نُمۡلِي لَهُمۡ خَيۡرٞ لِّأَنفُسِهِمۡۚ إِنَّمَا نُمۡلِي لَهُمۡ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِثۡمٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa.



الصفحة التالية
Icon