أَلَمۡ يَرَوۡاْ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّن قَرۡنٖ مَّكَّنَّـٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَا لَمۡ نُمَكِّن لَّكُمۡ وَأَرۡسَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡهِم مِّدۡرَارٗا وَجَعَلۡنَا ٱلۡأَنۡهَٰرَ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قَرۡنًا ءَاخَرِينَ

Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?


وَلَوۡ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ كِتَٰبٗا فِي قِرۡطَاسٖ فَلَمَسُوهُ بِأَيۡدِيهِمۡ لَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne."


وَقَالُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ مَلَكٞۖ وَلَوۡ أَنزَلۡنَا مَلَكٗا لَّقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ ثُمَّ لَا يُنظَرُونَ

Suka ce: "Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.


وَلَوۡ جَعَلۡنَٰهُ مَلَكٗا لَّجَعَلۡنَٰهُ رَجُلٗا وَلَلَبَسۡنَا عَلَيۡهِم مَّا يَلۡبِسُونَ

Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa.



الصفحة التالية
Icon