۞إِنَّمَا يَسۡتَجِيبُ ٱلَّذِينَ يَسۡمَعُونَۘ وَٱلۡمَوۡتَىٰ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ ثُمَّ إِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ

Abin sani kawai, waɗanda suke saurare ne suke karɓãwa, kuma matattu Allah Yake tãyar da su, Sa'an nan kuma zuwa gare Shi ake mayar da su.


وَقَالُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يُنَزِّلَ ءَايَةٗ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da ãyã ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ãyã, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba."


وَمَا مِن دَآبَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا طَـٰٓئِرٖ يَطِيرُ بِجَنَاحَيۡهِ إِلَّآ أُمَمٌ أَمۡثَالُكُمۚ مَّا فَرَّطۡنَا فِي ٱلۡكِتَٰبِ مِن شَيۡءٖۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ يُحۡشَرُونَ

Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa kuma bãbu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa fãce al'umma ne misãlanku. Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tãra su.


وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا صُمّٞ وَبُكۡمٞ فِي ٱلظُّلُمَٰتِۗ مَن يَشَإِ ٱللَّهُ يُضۡلِلۡهُ وَمَن يَشَأۡ يَجۡعَلۡهُ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ãyõyinMu, kurãme ne kuma bebãye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yanã ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya.



الصفحة التالية
Icon