قُل لَّآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ إِنِّي مَلَكٌۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّۚ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُۚ أَفَلَا تَتَفَكَّرُونَ
Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?"
وَأَنذِرۡ بِهِ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحۡشَرُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ لَيۡسَ لَهُم مِّن دُونِهِۦ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa.
وَلَا تَطۡرُدِ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ مَا عَلَيۡكَ مِنۡ حِسَابِهِم مِّن شَيۡءٖ وَمَا مِنۡ حِسَابِكَ عَلَيۡهِم مِّن شَيۡءٖ فَتَطۡرُدَهُمۡ فَتَكُونَ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma kada ka kõri waɗanda suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.
وَكَذَٰلِكَ فَتَنَّا بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لِّيَقُولُوٓاْ أَهَـٰٓؤُلَآءِ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنۢ بَيۡنِنَآۗ أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِٱلشَّـٰكِرِينَ
Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya?