بِئۡسَمَا ٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡ أَن يَكۡفُرُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بَغۡيًا أَن يُنَزِّلَ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ فَبَآءُو بِغَضَبٍ عَلَىٰ غَضَبٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci; kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa.


وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ ءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ نُؤۡمِنُ بِمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَيَكۡفُرُونَ بِمَا وَرَآءَهُۥ وَهُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَهُمۡۗ قُلۡ فَلِمَ تَقۡتُلُونَ أَنۢبِيَآءَ ٱللَّهِ مِن قَبۡلُ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"


۞وَلَقَدۡ جَآءَكُم مُّوسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.



الصفحة التالية
Icon