وَرَبُّكَ ٱلۡغَنِيُّ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفۡ مِنۢ بَعۡدِكُم مَّا يَشَآءُ كَمَآ أَنشَأَكُم مِّن ذُرِّيَّةِ قَوۡمٍ ءَاخَرِينَ

Kuma Ubangijinika Wadãtacce ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.


إِنَّ مَا تُوعَدُونَ لَأٓتٖۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ

Lalle ne abin da ake yi muku wa'adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba,


قُلۡ يَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَامِلٞۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba."


وَجَعَلُواْ لِلَّهِ مِمَّا ذَرَأَ مِنَ ٱلۡحَرۡثِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ نَصِيبٗا فَقَالُواْ هَٰذَا لِلَّهِ بِزَعۡمِهِمۡ وَهَٰذَا لِشُرَكَآئِنَاۖ فَمَا كَانَ لِشُرَكَآئِهِمۡ فَلَا يَصِلُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَا كَانَ لِلَّهِ فَهُوَ يَصِلُ إِلَىٰ شُرَكَآئِهِمۡۗ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan



الصفحة التالية
Icon