وَلَوۡ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَمَثُوبَةٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ خَيۡرٞۚ لَّوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani.


يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقُولُواْ رَٰعِنَا وَقُولُواْ ٱنظُرۡنَا وَٱسۡمَعُواْۗ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã' kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.


مَّا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَلَا ٱلۡمُشۡرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيۡكُم مِّنۡ خَيۡرٖ مِّن رَّبِّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَخۡتَصُّ بِرَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne.


۞مَا نَنسَخۡ مِنۡ ءَايَةٍ أَوۡ نُنسِهَا نَأۡتِ بِخَيۡرٖ مِّنۡهَآ أَوۡ مِثۡلِهَآۗ أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Abin da Muka shãfe daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?



الصفحة التالية
Icon