قَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ

Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne."


وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتۡنَاۚ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَتَوَفَّنَا مُسۡلِمِينَ

"Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! "


وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوۡمَهُۥ لِيُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَنَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡ وَإِنَّا فَوۡقَهُمۡ قَٰهِرُونَ

Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne."


قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱللَّهِ وَٱصۡبِرُوٓاْۖ إِنَّ ٱلۡأَرۡضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ

Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce."



الصفحة التالية
Icon