وَلِلَّهِ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ فَٱدۡعُوهُ بِهَاۖ وَذَرُواْ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ أَسۡمَـٰٓئِهِۦۚ سَيُجۡزَوۡنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.


وَمِمَّنۡ خَلَقۡنَآ أُمَّةٞ يَهۡدُونَ بِٱلۡحَقِّ وَبِهِۦ يَعۡدِلُونَ

Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci.


وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَنَسۡتَدۡرِجُهُم مِّنۡ حَيۡثُ لَا يَعۡلَمُونَ

Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.


وَأُمۡلِي لَهُمۡۚ إِنَّ كَيۡدِي مَتِينٌ

Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.


أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٌ

Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu? shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.


أَوَلَمۡ يَنظُرُواْ فِي مَلَكُوتِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٖ وَأَنۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَدِ ٱقۡتَرَبَ أَجَلُهُمۡۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ

Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?



الصفحة التالية
Icon