يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّمَن فِيٓ أَيۡدِيكُم مِّنَ ٱلۡأَسۡرَىٰٓ إِن يَعۡلَمِ ٱللَّهُ فِي قُلُوبِكُمۡ خَيۡرٗا يُؤۡتِكُمۡ خَيۡرٗا مِّمَّآ أُخِذَ مِنكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."


وَإِن يُرِيدُواْ خِيَانَتَكَ فَقَدۡ خَانُواْ ٱللَّهَ مِن قَبۡلُ فَأَمۡكَنَ مِنۡهُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ

Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.


إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُوٓاْ أُوْلَـٰٓئِكَ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَمۡ يُهَاجِرُواْ مَا لَكُم مِّن وَلَٰيَتِهِم مِّن شَيۡءٍ حَتَّىٰ يُهَاجِرُواْۚ وَإِنِ ٱسۡتَنصَرُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ فَعَلَيۡكُمُ ٱلنَّصۡرُ إِلَّا عَلَىٰ قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٞۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.



الصفحة التالية
Icon