وَكَذَٰلِكَ يَجۡتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَعَلَىٰٓ ءَالِ يَعۡقُوبَ كَمَآ أَتَمَّهَا عَلَىٰٓ أَبَوَيۡكَ مِن قَبۡلُ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

"Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."


۞لَّقَدۡ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخۡوَتِهِۦٓ ءَايَٰتٞ لِّلسَّآئِلِينَ

Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dõmin mãsu tambaya.


إِذۡ قَالُواْ لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰٓ أَبِينَا مِنَّا وَنَحۡنُ عُصۡبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.


ٱقۡتُلُواْ يُوسُفَ أَوِ ٱطۡرَحُوهُ أَرۡضٗا يَخۡلُ لَكُمۡ وَجۡهُ أَبِيكُمۡ وَتَكُونُواْ مِنۢ بَعۡدِهِۦ قَوۡمٗا صَٰلِحِينَ

Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.



الصفحة التالية
Icon