فَلَمَّا سَمِعَتۡ بِمَكۡرِهِنَّ أَرۡسَلَتۡ إِلَيۡهِنَّ وَأَعۡتَدَتۡ لَهُنَّ مُتَّكَـٔٗا وَءَاتَتۡ كُلَّ وَٰحِدَةٖ مِّنۡهُنَّ سِكِّينٗا وَقَالَتِ ٱخۡرُجۡ عَلَيۡهِنَّۖ فَلَمَّا رَأَيۡنَهُۥٓ أَكۡبَرۡنَهُۥ وَقَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّ وَقُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا مَلَكٞ كَرِيمٞ

Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!"


قَالَتۡ فَذَٰلِكُنَّ ٱلَّذِي لُمۡتُنَّنِي فِيهِۖ وَلَقَدۡ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفۡسِهِۦ فَٱسۡتَعۡصَمَۖ وَلَئِن لَّمۡ يَفۡعَلۡ مَآ ءَامُرُهُۥ لَيُسۡجَنَنَّ وَلَيَكُونٗا مِّنَ ٱلصَّـٰغِرِينَ

Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu."


قَالَ رَبِّ ٱلسِّجۡنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِۖ وَإِلَّا تَصۡرِفۡ عَنِّي كَيۡدَهُنَّ أَصۡبُ إِلَيۡهِنَّ وَأَكُن مِّنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."



الصفحة التالية
Icon