يُوسُفُ أَيُّهَا ٱلصِّدِّيقُ أَفۡتِنَا فِي سَبۡعِ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعِ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖ لَّعَلِّيٓ أَرۡجِعُ إِلَى ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَعۡلَمُونَ

"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."


قَالَ تَزۡرَعُونَ سَبۡعَ سِنِينَ دَأَبٗا فَمَا حَصَدتُّمۡ فَذَرُوهُ فِي سُنۢبُلِهِۦٓ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تَأۡكُلُونَ

Ya ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, sai kaɗan daga abin da kuke ci."


ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ سَبۡعٞ شِدَادٞ يَأۡكُلۡنَ مَا قَدَّمۡتُمۡ لَهُنَّ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تُحۡصِنُونَ

"Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa."


ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَامٞ فِيهِ يُغَاثُ ٱلنَّاسُ وَفِيهِ يَعۡصِرُونَ

"Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha."



الصفحة التالية
Icon