فَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمۡ جَعَلَ ٱلسِّقَايَةَ فِي رَحۡلِ أَخِيهِ ثُمَّ أَذَّنَ مُؤَذِّنٌ أَيَّتُهَا ٱلۡعِيرُ إِنَّكُمۡ لَسَٰرِقُونَ

Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne."


قَالُواْ وَأَقۡبَلُواْ عَلَيۡهِم مَّاذَا تَفۡقِدُونَ

Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: "Mẽne ne kuke nẽma?"


قَالُواْ نَفۡقِدُ صُوَاعَ ٱلۡمَلِكِ وَلِمَن جَآءَ بِهِۦ حِمۡلُ بَعِيرٖ وَأَنَا۠ بِهِۦ زَعِيمٞ

Suka ce: "Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi."


قَالُواْ تَٱللَّهِ لَقَدۡ عَلِمۡتُم مَّا جِئۡنَا لِنُفۡسِدَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا كُنَّا سَٰرِقِينَ

Suka ce: "Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba."


قَالُواْ فَمَا جَزَـٰٓؤُهُۥٓ إِن كُنتُمۡ كَٰذِبِينَ

Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?"


قَالُواْ جَزَـٰٓؤُهُۥ مَن وُجِدَ فِي رَحۡلِهِۦ فَهُوَ جَزَـٰٓؤُهُۥۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ

Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai."



الصفحة التالية
Icon