يَٰبَنِيَّ ٱذۡهَبُواْ فَتَحَسَّسُواْ مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلَا تَاْيۡـَٔسُواْ مِن رَّوۡحِ ٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ لَا يَاْيۡـَٔسُ مِن رَّوۡحِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

"Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai."


فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَيۡهِ قَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهۡلَنَا ٱلضُّرُّ وَجِئۡنَا بِبِضَٰعَةٖ مُّزۡجَىٰةٖ فَأَوۡفِ لَنَا ٱلۡكَيۡلَ وَتَصَدَّقۡ عَلَيۡنَآۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَجۡزِي ٱلۡمُتَصَدِّقِينَ

Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. "


قَالَ هَلۡ عَلِمۡتُم مَّا فَعَلۡتُم بِيُوسُفَ وَأَخِيهِ إِذۡ أَنتُمۡ جَٰهِلُونَ

Ya ce: "Shin, kan san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?"


قَالُوٓاْ أَءِنَّكَ لَأَنتَ يُوسُفُۖ قَالَ أَنَا۠ يُوسُفُ وَهَٰذَآ أَخِيۖ قَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَآۖ إِنَّهُۥ مَن يَتَّقِ وَيَصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa."



الصفحة التالية
Icon