وَمَا يُؤۡمِنُ أَكۡثَرُهُم بِٱللَّهِ إِلَّا وَهُم مُّشۡرِكُونَ
Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki.
أَفَأَمِنُوٓاْ أَن تَأۡتِيَهُمۡ غَٰشِيَةٞ مِّنۡ عَذَابِ ٱللَّهِ أَوۡ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin ¡iyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?
قُلۡ هَٰذِهِۦ سَبِيلِيٓ أَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِيۖ وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Ka ce: "Wannan ce hanyãta; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰٓۗ أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۗ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?