وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau.
جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّـٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَدۡخُلُونَ عَلَيۡهِم مِّن كُلِّ بَابٖ
Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa.
سَلَٰمٌ عَلَيۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
"Aminci ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida."
وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ
Kuma waɗanda suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida.