فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.


وَقَٰتِلُوهُمۡ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتۡنَةٞ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ لِلَّهِۖ فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَلَا عُدۡوَٰنَ إِلَّا عَلَى ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma ku yãƙe su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.


ٱلشَّهۡرُ ٱلۡحَرَامُ بِٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ وَٱلۡحُرُمَٰتُ قِصَاصٞۚ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَٱعۡتَدُواْ عَلَيۡهِ بِمِثۡلِ مَا ٱعۡتَدَىٰ عَلَيۡكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُتَّقِينَ

Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa.


وَأَنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا تُلۡقُواْ بِأَيۡدِيكُمۡ إِلَى ٱلتَّهۡلُكَةِ وَأَحۡسِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ku ciyar a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.


وَأَتِمُّواْ ٱلۡحَجَّ وَٱلۡعُمۡرَةَ لِلَّهِۚ فَإِنۡ أُحۡصِرۡتُمۡ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۖ وَلَا تَحۡلِقُواْ رُءُوسَكُمۡ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡهَدۡيُ مَحِلَّهُۥۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ بِهِۦٓ أَذٗى مِّن رَّأۡسِهِۦ فَفِدۡيَةٞ مِّن صِيَامٍ أَوۡ صَدَقَةٍ أَوۡ نُسُكٖۚ فَإِذَآ أَمِنتُمۡ فَمَن تَمَتَّعَ بِٱلۡعُمۡرَةِ إِلَى ٱلۡحَجِّ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۚ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖ فِي ٱلۡحَجِّ وَسَبۡعَةٍ إِذَا رَجَعۡتُمۡۗ تِلۡكَ عَشَرَةٞ كَامِلَةٞۗ ذَٰلِكَ لِمَن لَّمۡ يَكُنۡ أَهۡلُهُۥ حَاضِرِي ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.



الصفحة التالية
Icon