قَالَ أَرَاغِبٌ أَنتَ عَنۡ ءَالِهَتِي يَـٰٓإِبۡرَٰهِيمُۖ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ لَأَرۡجُمَنَّكَۖ وَٱهۡجُرۡنِي مَلِيّٗا

Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci."


قَالَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكَۖ سَأَسۡتَغۡفِرُ لَكَ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ بِي حَفِيّٗا

Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni."


وَأَعۡتَزِلُكُمۡ وَمَا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَأَدۡعُواْ رَبِّي عَسَىٰٓ أَلَّآ أَكُونَ بِدُعَآءِ رَبِّي شَقِيّٗا

"Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina."


فَلَمَّا ٱعۡتَزَلَهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا نَبِيّٗا

To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi.


وَوَهَبۡنَا لَهُم مِّن رَّحۡمَتِنَا وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ لِسَانَ صِدۡقٍ عَلِيّٗا

Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya maɗaukaki.



الصفحة التالية
Icon