وَهَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?
إِذۡ رَءَا نَارٗا فَقَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِقَبَسٍ أَوۡ أَجِدُ عَلَى ٱلنَّارِ هُدٗى
A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar."
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ يَٰمُوسَىٰٓ
Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!"
إِنِّيٓ أَنَا۠ رَبُّكَ فَٱخۡلَعۡ نَعۡلَيۡكَ إِنَّكَ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوٗى
"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa."
وَأَنَا ٱخۡتَرۡتُكَ فَٱسۡتَمِعۡ لِمَا يُوحَىٰٓ
"Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi."
إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ
"Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni."