قَالَ فَمَا بَالُ ٱلۡقُرُونِ ٱلۡأُولَىٰ

Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?"


قَالَ عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَٰبٖۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى

Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa."


ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَسَلَكَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّن نَّبَاتٖ شَتَّىٰ

"Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam.


كُلُواْ وَٱرۡعَوۡاْ أَنۡعَٰمَكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ

Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali.


۞مِنۡهَا خَلَقۡنَٰكُمۡ وَفِيهَا نُعِيدُكُمۡ وَمِنۡهَا نُخۡرِجُكُمۡ تَارَةً أُخۡرَىٰ

Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam.


وَلَقَدۡ أَرَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَىٰ

Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya!



الصفحة التالية
Icon