فَلَمَّآ أَحَسُّواْ بَأۡسَنَآ إِذَا هُم مِّنۡهَا يَرۡكُضُونَ

Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta.


لَا تَرۡكُضُواْ وَٱرۡجِعُوٓاْ إِلَىٰ مَآ أُتۡرِفۡتُمۡ فِيهِ وَمَسَٰكِنِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُسۡـَٔلُونَ

"Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku."


قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ

Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."


فَمَا زَالَت تِّلۡكَ دَعۡوَىٰهُمۡ حَتَّىٰ جَعَلۡنَٰهُمۡ حَصِيدًا خَٰمِدِينَ

Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu.


وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا لَٰعِبِينَ

Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba.


لَوۡ أَرَدۡنَآ أَن نَّتَّخِذَ لَهۡوٗا لَّٱتَّخَذۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّآ إِن كُنَّا فَٰعِلِينَ

Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.


بَلۡ نَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَى ٱلۡبَٰطِلِ فَيَدۡمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٞۚ وَلَكُمُ ٱلۡوَيۡلُ مِمَّا تَصِفُونَ

Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa.



الصفحة التالية
Icon