وَنُوحًا إِذۡ نَادَىٰ مِن قَبۡلُ فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ

Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma.


وَنَصَرۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمَ سَوۡءٖ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ أَجۡمَعِينَ

Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.


وَدَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ إِذۡ يَحۡكُمَانِ فِي ٱلۡحَرۡثِ إِذۡ نَفَشَتۡ فِيهِ غَنَمُ ٱلۡقَوۡمِ وَكُنَّا لِحُكۡمِهِمۡ شَٰهِدِينَ

Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu.


فَفَهَّمۡنَٰهَا سُلَيۡمَٰنَۚ وَكُلًّا ءَاتَيۡنَا حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَسَخَّرۡنَا مَعَ دَاوُۥدَ ٱلۡجِبَالَ يُسَبِّحۡنَ وَٱلطَّيۡرَۚ وَكُنَّا فَٰعِلِينَ

Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.


وَعَلَّمۡنَٰهُ صَنۡعَةَ لَبُوسٖ لَّكُمۡ لِتُحۡصِنَكُم مِّنۢ بَأۡسِكُمۡۖ فَهَلۡ أَنتُمۡ شَٰكِرُونَ

Kuma Muka sanar da shi sana'ar wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?



الصفحة التالية
Icon