وَأَدۡخَلۡنَٰهُمۡ فِي رَحۡمَتِنَآۖ إِنَّهُم مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai.


وَذَا ٱلنُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَٰضِبٗا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقۡدِرَ عَلَيۡهِ فَنَادَىٰ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ أَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبۡحَٰنَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma mai kifi a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."


فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡغَمِّۚ وَكَذَٰلِكَ نُـۨجِي ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni.


وَزَكَرِيَّآ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ رَبِّ لَا تَذَرۡنِي فَرۡدٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡوَٰرِثِينَ

Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo."


فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَوَهَبۡنَا لَهُۥ يَحۡيَىٰ وَأَصۡلَحۡنَا لَهُۥ زَوۡجَهُۥٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَيَدۡعُونَنَا رَغَبٗا وَرَهَبٗاۖ وَكَانُواْ لَنَا خَٰشِعِينَ

Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu.



الصفحة التالية
Icon