وَٱقۡتَرَبَ ٱلۡوَعۡدُ ٱلۡحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَٰخِصَةٌ أَبۡصَٰرُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَٰوَيۡلَنَا قَدۡ كُنَّا فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا بَلۡ كُنَّا ظَٰلِمِينَ

Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"


إِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ

(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."


لَوۡ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةٗ مَّا وَرَدُوهَاۖ وَكُلّٞ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.


لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَهُمۡ فِيهَا لَا يَسۡمَعُونَ

Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.


إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتۡ لَهُم مِّنَّا ٱلۡحُسۡنَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ عَنۡهَا مُبۡعَدُونَ

Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.



الصفحة التالية
Icon