وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.


قُلۡ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?"


فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ ءَاذَنتُكُمۡ عَلَىٰ سَوَآءٖۖ وَإِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٌ أَم بَعِيدٞ مَّا تُوعَدُونَ

Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?"


إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡتُمُونَ

"Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa.


وَإِنۡ أَدۡرِي لَعَلَّهُۥ فِتۡنَةٞ لَّكُمۡ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ

"Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci."


قَٰلَ رَبِّ ٱحۡكُم بِٱلۡحَقِّۗ وَرَبُّنَا ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلۡمُسۡتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ

Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa."



الصفحة التالية
Icon