وَقَوۡمُ إِبۡرَٰهِيمَ وَقَوۡمُ لُوطٖ

Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu.


وَأَصۡحَٰبُ مَدۡيَنَۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰۖ فَأَمۡلَيۡتُ لِلۡكَٰفِرِينَ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa (gare su) ya kasance?


فَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ فَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَبِئۡرٖ مُّعَطَّلَةٖ وَقَصۡرٖ مَّشِيدٍ

Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka.


أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَتَكُونَ لَهُمۡ قُلُوبٞ يَعۡقِلُونَ بِهَآ أَوۡ ءَاذَانٞ يَسۡمَعُونَ بِهَاۖ فَإِنَّهَا لَا تَعۡمَى ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَلَٰكِن تَعۡمَى ٱلۡقُلُوبُ ٱلَّتِي فِي ٱلصُّدُورِ

Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta.


وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥۚ وَإِنَّ يَوۡمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلۡفِ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa.



الصفحة التالية
Icon