وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa.


وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓاْ أَوۡ مَاتُواْ لَيَرۡزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa.


لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri.


۞ذَٰلِكَۖ وَمَنۡ عَاقَبَ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيۡهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.


ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani.



الصفحة التالية
Icon