حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَوۡاْ عَلَىٰ وَادِ ٱلنَّمۡلِ قَالَتۡ نَمۡلَةٞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّمۡلُ ٱدۡخُلُواْ مَسَٰكِنَكُمۡ لَا يَحۡطِمَنَّكُمۡ سُلَيۡمَٰنُ وَجُنُودُهُۥ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."


فَتَبَسَّمَ ضَاحِكٗا مِّن قَوۡلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَدۡخِلۡنِي بِرَحۡمَتِكَ فِي عِبَادِكَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."


وَتَفَقَّدَ ٱلطَّيۡرَ فَقَالَ مَالِيَ لَآ أَرَى ٱلۡهُدۡهُدَ أَمۡ كَانَ مِنَ ٱلۡغَآئِبِينَ

Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"


لَأُعَذِّبَنَّهُۥ عَذَابٗا شَدِيدًا أَوۡ لَأَاْذۡبَحَنَّهُۥٓ أَوۡ لَيَأۡتِيَنِّي بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ

"Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne."



الصفحة التالية
Icon