فَلَمَّا جَآءَتۡ قِيلَ أَهَٰكَذَا عَرۡشُكِۖ قَالَتۡ كَأَنَّهُۥ هُوَۚ وَأُوتِينَا ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهَا وَكُنَّا مُسۡلِمِينَ

To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)."


وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعۡبُدُ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ إِنَّهَا كَانَتۡ مِن قَوۡمٖ كَٰفِرِينَ

Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai.


قِيلَ لَهَا ٱدۡخُلِي ٱلصَّرۡحَۖ فَلَمَّا رَأَتۡهُ حَسِبَتۡهُ لُجَّةٗ وَكَشَفَتۡ عَن سَاقَيۡهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرۡحٞ مُّمَرَّدٞ مِّن قَوَارِيرَۗ قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي وَأَسۡلَمۡتُ مَعَ سُلَيۡمَٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu."



الصفحة التالية
Icon