فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّفۡتَرٗى وَمَا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ
To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ مِنۡ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."
وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ مَا عَلِمۡتُ لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرِي فَأَوۡقِدۡ لِي يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجۡعَل لِّي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."
وَٱسۡتَكۡبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ إِلَيۡنَا لَا يُرۡجَعُونَ
Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.