وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?"
قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغۡوَيۡنَآ أَغۡوَيۡنَٰهُمۡ كَمَا غَوَيۡنَاۖ تَبَرَّأۡنَآ إِلَيۡكَۖ مَا كَانُوٓاْ إِيَّانَا يَعۡبُدُونَ
Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba."
وَقِيلَ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ لَوۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ يَهۡتَدُونَ
Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa!
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ مَاذَآ أَجَبۡتُمُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?"
فَعَمِيَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَنۢبَآءُ يَوۡمَئِذٖ فَهُمۡ لَا يَتَسَآءَلُونَ
Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnaosu ba.