تِلۡكَ ٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ نَجۡعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوّٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فَسَادٗاۚ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ

Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.


مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.


إِنَّ ٱلَّذِي فَرَضَ عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٖۚ قُل رَّبِّيٓ أَعۡلَمُ مَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ وَمَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananna."


وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako ga kãfirai.



الصفحة التالية
Icon