وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلۡمُجۡرِمُونَ نَاكِسُواْ رُءُوسِهِمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ رَبَّنَآ أَبۡصَرۡنَا وَسَمِعۡنَا فَٱرۡجِعۡنَا نَعۡمَلۡ صَٰلِحًا إِنَّا مُوقِنُونَ

Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne."


وَلَوۡ شِئۡنَا لَأٓتَيۡنَا كُلَّ نَفۡسٍ هُدَىٰهَا وَلَٰكِنۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ مِنِّي لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya.


فَذُوقُواْ بِمَا نَسِيتُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَآ إِنَّا نَسِينَٰكُمۡۖ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡخُلۡدِ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.


إِنَّمَا يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِهَا خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَسَبَّحُواْ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ۩

Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai.



الصفحة التالية
Icon