۞قُلۡ يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسۡرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُواْ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
وَأَنِيبُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَأَسۡلِمُواْ لَهُۥ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ
"Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba."
وَٱتَّبِعُوٓاْ أَحۡسَنَ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ بَغۡتَةٗ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ
"Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba."
أَن تَقُولَ نَفۡسٞ يَٰحَسۡرَتَىٰ عَلَىٰ مَا فَرَّطتُ فِي جَنۢبِ ٱللَّهِ وَإِن كُنتُ لَمِنَ ٱلسَّـٰخِرِينَ
"Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!"'
أَوۡ تَقُولَ لَوۡ أَنَّ ٱللَّهَ هَدَىٰنِي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ
"Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'"