۞وَقَيَّضۡنَا لَهُمۡ قُرَنَآءَ فَزَيَّنُواْ لَهُم مَّا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَحَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ

Kuma Muka sallaɗar da mabiya a gare su, sai suka ƙawãta musu abin da ke a gabansu da abin da ke a bãyansu. Kuma kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin wasu al'ummõmi da suka shũɗe a gabãninsu daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.


وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَسۡمَعُواْ لِهَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ وَٱلۡغَوۡاْ فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَغۡلِبُونَ

Kuma waɗanda suka kafirta suka cc, "Kada ku saurãra ga wannan Alkur' ãni, kuma ku yi ta yin kuwwa a ckin (lõkacin karãtun) sa, ɗammãninku zã ku rinjaya."


فَلَنُذِيقَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَذَابٗا شَدِيدٗا وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَسۡوَأَ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sabõda haka, lalle zã Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azãba mai tsanani, kuma lalle zã Mu sãka musu da mafi mũnin abin da suka kasance sunã aikatãwa.


ذَٰلِكَ جَزَآءُ أَعۡدَآءِ ٱللَّهِ ٱلنَّارُۖ لَهُمۡ فِيهَا دَارُ ٱلۡخُلۡدِ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ

Wancan shĩ ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Sunã a gidan dawwama a cikinta, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã yin musu game da ãyõyinMu.



الصفحة التالية
Icon