وَلَئِنۡ أَذَقۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنَّا مِنۢ بَعۡدِ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُ لَيَقُولَنَّ هَٰذَا لِي وَمَآ أَظُنُّ ٱلسَّاعَةَ قَآئِمَةٗ وَلَئِن رُّجِعۡتُ إِلَىٰ رَبِّيٓ إِنَّ لِي عِندَهُۥ لَلۡحُسۡنَىٰۚ فَلَنُنَبِّئَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِمَا عَمِلُواْ وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنۡ عَذَابٍ غَلِيظٖ

Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurinSa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri.


وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ فَذُو دُعَآءٍ عَرِيضٖ

Kuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi.


قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ ثُمَّ كَفَرۡتُم بِهِۦ مَنۡ أَضَلُّ مِمَّنۡ هُوَ فِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

Ka ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?"



الصفحة التالية
Icon