وَتَرَىٰهُمۡ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا خَٰشِعِينَ مِنَ ٱلذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرۡفٍ خَفِيّٖۗ وَقَالَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ ٱلۡخَٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَأَهۡلِيهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَآ إِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ فِي عَذَابٖ مُّقِيمٖ

Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, "Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar ¡iyãma." To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya.


وَمَا كَانَ لَهُم مِّنۡ أَوۡلِيَآءَ يَنصُرُونَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن سَبِيلٍ

Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra.


ٱسۡتَجِيبُواْ لِرَبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۚ مَا لَكُم مِّن مَّلۡجَإٖ يَوۡمَئِذٖ وَمَا لَكُم مِّن نَّكِيرٖ

Ku karɓã wa Ubangijinku tun gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare shi daga Allah, bã ku da wata mafaka a rãnar nan, kuma bã ku iya yin wani musu.


فَإِنۡ أَعۡرَضُواْ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظًاۖ إِنۡ عَلَيۡكَ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُۗ وَإِنَّآ إِذَآ أَذَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِنَّا رَحۡمَةٗ فَرِحَ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ فَإِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ كَفُورٞ

To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne.



الصفحة التالية
Icon