قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ وَكَفَرۡتُم بِهِۦ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَلَىٰ مِثۡلِهِۦ فَـَٔامَنَ وَٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."


وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَوۡ كَانَ خَيۡرٗا مَّا سَبَقُونَآ إِلَيۡهِۚ وَإِذۡ لَمۡ يَهۡتَدُواْ بِهِۦ فَسَيَقُولُونَ هَٰذَآ إِفۡكٞ قَدِيمٞ

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur'ãni) ya kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe."


وَمِن قَبۡلِهِۦ كِتَٰبُ مُوسَىٰٓ إِمَامٗا وَرَحۡمَةٗۚ وَهَٰذَا كِتَٰبٞ مُّصَدِّقٞ لِّسَانًا عَرَبِيّٗا لِّيُنذِرَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُحۡسِنِينَ

Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa.



الصفحة التالية
Icon