أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ نَتَقَبَّلُ عَنۡهُمۡ أَحۡسَنَ مَا عَمِلُواْ وَنَتَجَاوَزُ عَن سَيِّـَٔاتِهِمۡ فِيٓ أَصۡحَٰبِ ٱلۡجَنَّةِۖ وَعۡدَ ٱلصِّدۡقِ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ
Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi).
وَٱلَّذِي قَالَ لِوَٰلِدَيۡهِ أُفّٖ لَّكُمَآ أَتَعِدَانِنِيٓ أَنۡ أُخۡرَجَ وَقَدۡ خَلَتِ ٱلۡقُرُونُ مِن قَبۡلِي وَهُمَا يَسۡتَغِيثَانِ ٱللَّهَ وَيۡلَكَ ءَامِنۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ فَيَقُولُ مَا هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ
Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.