سَيَهۡدِيهِمۡ وَيُصۡلِحُ بَالَهُمۡ

Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu.


وَيُدۡخِلُهُمُ ٱلۡجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمۡ

Kuma Ya shigarda su Aljanna (wadda) Ya siffanta ta a gare su.


يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تَنصُرُواْ ٱللَّهَ يَنصُرۡكُمۡ وَيُثَبِّتۡ أَقۡدَامَكُمۡ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..


وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَتَعۡسٗا لَّهُمۡ وَأَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.


ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَرِهُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu.


۞أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ دَمَّرَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۖ وَلِلۡكَٰفِرِينَ أَمۡثَٰلُهَا

Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).



الصفحة التالية
Icon