Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni*. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.
____________________
* Idan an umurci mutum ya rabu da ubansa da 'yan'uwansa kãfirai, sabõda shĩ yanã Musulmi, to, ga waninsu abin yã fi ƙarfi.