Ku yãƙi waɗanda* bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.
____________________
* Bãyan gama hukuncin alãƙar Musulmi da kãfiran farko, watau mãsu shirkin, Lãrabãwa, sai kuma ya fãra bayãnin alãƙar Musulmi kãfirai na biyu; watau Yahũdu da Nasãra.