Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi* zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.
____________________
* Nauyi zuwa ga ƙasa, watau ku ƙãsa tãshi tsaye balle mã ku fita zuwa yãƙin da aka neme ku da shi (sabõda shi). fita da yãƙi a nan, anã nufin yãƙin Tabũka a cikin lõkacin bazara, kuma bãbu abinci dõmin Allah Ya jarrabi Musulmi, Ya fitar da mũminai da kuma munãfukai, dõmin a san yadda zã a yi ma'ãmala da su. Haka kuma a kõwane lõkaci Allah Yakan sanya wani abin jarraba na wahala a cikin Musulmi dõmin Ya bambanta mũminai daga munãfukai.