Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama* ba fãce yanã a cikin ɓata.
____________________
* Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗanda kõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã neman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa.